Matthew 24

1Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali. 2Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za’a bari akan dan’uwansa wanda ba za’a rushe shi ba.”

3Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, “me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?” 4Yesu ya amsa yace dasu, “Ku kula kada wani yasa ku kauce.” 5Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, “ni ne almasihu,” kuma za su sa da yawa su kauce.

6Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna. 7Gama al’umma zata tayarwa al’umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za’a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. 8Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai.

9Bayan haka za’a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al’ummai za su tsane ku saboda sunana. 10Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna. 11Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce.

12Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi. 13Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto. 14Za’a yi wa’azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al’ummai. Daganan karshen zai zo.

15Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta), 16bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu, 17Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa, 18kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa.

19Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin! 20Ku yi addu’a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci. 21Domin za’ayi tsanani mai girma, wanda ba’a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a’a ba za ayi irin shi ba kuma. 22In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin.

23Sa’annan idan wani yace maku, duba, “ga Almasihu a nan!” ko, “ga Almasihu a can!” kar ku gaskata. 24Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al’ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. 25Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo.

26Saboda haka, idan suka ce maku, “ga shi a jeji,” kar ku je jejin. Ko, “ga shi a can cikin kuryar daki,” kar ku gaskata. 27Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama. 28Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa.

29Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza.

30Sa’annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma. 31Zai aiki mala’ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen.

32Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa. 33Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa.

34Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru. 35Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba.

36Amma game da ranan nan ko sa’a ba wanda ya sani, ko mala’ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai.

37Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum. 38A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin, 39ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su_ haka ma zuwan Dan Mutun zai zama.

40Sa’annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya. 41Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar. 42Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba.

43Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba. 44Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi zato ba.

45To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci? 46Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo. 47Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi.

48Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, “maigida na ya yi jinkiri,” 49sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya, 50uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba. Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.

51

Copyright information for HauULB